June 7, 2024

kimanin mutune miliyan 12 ne aka tilastawa barin gidajensu a Sudan,

Yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Darfur na arewacin Sudan, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta yi gargadi a cikin wata sanarwa cewa “yawan mutanen da rikicin Sudan ya raba da muhallansu zai iya haura miliyan 10 nan da kwanaki masu zuwa.”

IOM ta kuma bayar da rahoton cewa, kimanin ‘yan Sudan miliyan 9.9 ne yanzu haka suke gudun hijira a duk yankuna 18 na Sudan, fiye da rabinsu mata ne kuma kashi daya bisa hudu na yara ‘yan kasa da shekaru biyar ne.

Sanarwar ta kara da cewa, “A dunkule, kimanin miliyan 12 ne aka tilastawa barin gidajensu a Sudan, tare da tsallaka kan iyakoki fiye da miliyan biyu zuwa kasashe makwabta, musamman Chadi, Sudan ta Kudu, da Masar,” in ji sanarwar.

www.ahlulbaiti.com

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “kimanin mutune miliyan 12 ne aka tilastawa barin gidajensu a Sudan,”