September 6, 2021

KIFAR DA GWAMNATI A GUINEA: Najeriya tayi Allah-wadai, Majalisar dinkin runiya ta nemi sakin Condé.

Daga Muhammad Bakir Muhammad

Gwamnatin Najeriya tayi Allah wadai da kifar da gwamnatin Alpha Conde na Tarayyar Guinea inda ta bayyana hakan a matsayin hawan kawara ga dokoki da sharrudan ECOWAS kana kuma tace hakan ya saba ma Demokradiyya. Ta kuma ce bata goyon bayan duk wani sauyin gwamnati da bai gudana ta hanyar kundin tsarin mulki ba kuma tayi kira ga masu ruwa da tsaki a wannan danyen aiki da su janye aniyar su ta hanyar martaba dokokin kundin tsarin mulki bisa salama ba tare da salwantar da wata rai ko dukiya ba.

A bangare guda kuma, Babban sakataren Majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya wallafa a shafin tuwiya inda yake kalubantar dukkan wani sauyin gwamnati ta hanyar karfin makamai, kana kuma ya nemi sakin Shugaba Alpha Conde cikin gaggawa.

Lamarin dai ya faru a yayin da wasu gamayyar sojoji karkashin shugabancin Kanal Mamady Doumbouya suka bude wuta a fadar gwamnatin kasar ta Guinea dake babban birnin kasar Conakry kana kuma sukayi awun gaba da shugaban kasa Alpha Conde inda daga baya suka bayyana aniyarsu na kifar da gwamnatin da kuma sauya ta da wata daban.

Wasu sun nuna yunkurin sojojin a matsayin martani ga kokarin da majalisar kasar take na kara albashin yan siyasan kasar da kuma zabtare albashin bangarorin tsaro.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “KIFAR DA GWAMNATI A GUINEA: Najeriya tayi Allah-wadai, Majalisar dinkin runiya ta nemi sakin Condé.”