March 27, 2023

KHUDUBAN MANZON (S.A.W.A) A WATAN RAMADAN.

 

Daga Amirul muminin (Aliyu bini Abi Talib (A.S) Yace: “Manzon Allah (S.A.W.A) yayi mana khuduba wata rana, sai yace: Ya ku mutane! Lalle watan Allah mai Albarka da Rahama da Gafara ya fuskanto gareku. Wata ne wanda yake mafificin watanni a wurin Allah, kwanakinsa mafificin kwanaki, darensa sune mafificin darare ku, sa’o’insa sune mafificin sa’o’i. wata ne wanda aka kira ku zuwa bakuntar Allah (liyafa) kuma an sanya ku cikin ma’abota karamcin Allah. Nunfashinku tasbihi ne, baccin ku kuma ibada ne, Kuma ai’kin ku Kuma karbabbe ne , ADDU’AN KU abin amsawa ne Don haka ku roki Allah da niyya ta gaskiya tare da zuciya tsarkakkiya ya datar daku ga yin azumi tare da karatun Al’kur’ani. Lalle shakiyi! Shine wanda aka haramta ma shi gafaran Allah a cikin wannan wata mai girma. Ku tuna da yun’warku da kishirwanku, yun’war ranar kiyama da kishirwanta! Kuyi sadaka wa fakirai da miskinan ku,ku girmama manyan ku, sannan kuji tausayin kananan ku. Ku sadar da zumuncin ku, ku kiyaye harshen ku, ku kame jinku daga abinda bai Halasta kuji ba! Ku tausasa wa marayun mutane, sai ku ma a tausasa wa marayunku.

Ku tuba zuwa ga Allah daga zunubanku,sannan ku daga hannuwanku da addu’a a lokutan sallanku domin wannan lokacin shine mafificin lokaci, Allah yana kallon bayin sa acikin sa da rahma. Idan sunyi munajati dashi Zai Basu, idan Kuma sun kira shi Zai Amsa musu, sannan kuma yana karba musu addu’a.Ya ku mutane! Lalle numfashinku abin jingina ne ga ai’yukanku, don haka ku fanso ranku da yin istigfari. Zunuban ku suna da nauyi, ku sau kake su da tsawaita sujjada wa Lalle, ku sani! Allah yayi ratsuwa da buwayansa akan cewa ba zai azabtar da masu sallah da sujjada ba acikin ku, kuma ba zai razanar dasu da wuta ba a ranar da mutane zasu tsaya a gaban ubangijin talikai .

Ya ku mutane! Lalle duk wanda ya bude bakin mai azumi mumini, a cikin wannan wata, to zai kasance yana da ladan wanda ya yan’tar da bawa a wurin Allah. Kuma za’a gafarta masa zunubansa wanda ya gabata. Sai akace: Ya manzon Allah, ba dukan mu ne muke da ikon yin haka ba? sai Manzon Allah (SAW) yace: Ku kare kan ku daga wuta! Ko da da tsagin dabino ne, kai koda kofin ruwa ne!” Ya ku mutane! Duk wanda ya kyautata halinsa a wannan wata, zai kasance yana da sheda ta tsallake siradi a ranar da kafafuwa suke zamewa. Duk wanda ya saukaka ma wanda suke karkashin sa, to, Allah zai saukake mashi hisabi, kuma duk wanda ya kama sharrinsa (daga mutane), Allah zai kame fushin sa akan shi a ranar gamuwa dashi. Kuma duk Wanda ya karrama maraya , Allah Zai karrama shi a ranar gamuwa dashi.Wanda kuma ya Sadar da Zumuncin sa, Allah Zai Sadar dashi ga rahamar Da. Wanda ya yanke zumuncin sa a cikin wannan wata, Allah zai yanke rahamar sa gare shi ranar kiyama.

Duk wanda yayi sallah ta nafila a cikin wannan wata, Allah zai rubuta masa kubuta daga wuta, wanda kuma ya ai’kata aiki na farilla zai kasance yana da ladan wanda yayi farilla saba’in(70) a cikin wani wata bana Ramadan ba, wanda kuma ya yawaita salati a gareni (Manzon Allah Saw), Allah zai Nauyaya mizaninsa a ranar da mizani suke sauki (rashin nauyi) wanda Kuma ya karanta aya daga cikin Al’kur’ani, zai kasance yana da lada na wanda ya sauke Al’kur’ani a cikin wani wata bana Ramadan ba. Yaku mutane! Lalle kofofin Al-jannah a bude suke a wannan wata, Ku roki Allah kada a rufe a kanku, (ba tare da kun shiga ba) kuma kofofin wuta a rufe suke, don haka ku roki Allah kada ya bude gareku (wato kuyi aikin da zaku shiga wuta) shaidanu fa a daure suke, don haka ku roki Allah kada ya salladasu akan ku.

Amirul muminina Aliyu (A.S) Yace: “sai na tashi nace: “Ya manzon Allah, menene mafificin ai’ki a cikin wannan wata ”? Manzon Allah (SAW) Yace: “Ya baban Hassan! Mafificin aiki a wannan wata shine: Tsantseni akan abinda Allah ya haramta.

 

SHARE:
Makala 0 Replies to “KHUDUBAN MANZON (S.A.W.A) A WATAN RAMADAN.”