KAWO GYARA DA DAIDAITO A LAMARIN GANIN WATA A NAJERIYA: KOMITIN GANIN WATA YA CANCANCI YABO.

Bayan fuskantar kalu bale da komitin ganin watan dake karkashin majalisar koli ta addinin musulunci na Najeriya da ke karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abukar yayi ta fuskanta na turjiya daga al’umma har da zage-zage, to a hankali har al’umma sun fara samun nitsuwa game da wannan lamari.
Kamawar watan Ramadhan na wannan shekara ta 1444/2023 ya nuna haka, sakamakon yanda mutane da dama suka nuna farin cikin su da yanayin kamawar watan, ta yanda ganin watan ya zama ya yadu mutane da yawa suna bada shaidar cewa sun ga watan babu tantama ko jirwaye-jirwaye da idanuwan su. Ba kamar yanda aka saba a baya ba, sai an dauki azumi biyu ko uku ko bayan karamar sallah da kwana biyu ko uku kafin a ga wata. Wanda hakan ke nuna cewa tabbas a baya an yi ta kura-kurai wajen daukan azumi a watan Sha’aban da kuma ajiyewa a watan Ramadhan (Allah Ta’ala Ya yafe mana), kuma sau da dama ana samun mune kasa daya tilo a duniya da muka fara azumi ko shan ruwa. Amma sai dayawan mutane suka dauka cewa wancan kirgen na baya shine daidai.
Shigar da ilimin kimiyyar falaki a cikin lamarin ya taimaka mun shiga sahun al’ummar duniyar zamanin yau wayayya.
Wannan rubutu da ke sama budaddiyar wasika ce da ni Murtala Isah Dass na rubuta na jinjinawa ga Mai alfarma Sarkin Musulmi a shekarar 2016 a jaridar takarda ta Ahlul Baiti, mallakar Rasulul A’azam Foundation (RAAF), sakamakon jajircewar shi Sarkin Musulmi a kan wannan gyara da ya kawo, amma al’ummar mu ta kasa fahimtarsa wanda hakan ya sabbaba masa bakin jini sosai, kama daga kan wasu malamai jagororin addini har da wasu sarakuna balle kuma sauran talakawa.
Na rubuta wannan makala ce tare da sahhalewa da karfafawar shugaban wannan mu’assasa tamu mai albarka RAAF Hujjatul Islam wal Muslimin Shaikh Muhammad Nura Dass (H)
Duk da cewa har yanzun ma haka mafi yawan jama’a suna husuma da wannan mataki, to amma dai ana samun sauki da karin fahimta.
Dama fada da cigaban zamani da ilimin kimiyya a wajen mu tamkar sunnah ce, sai an yi ta fama, balle kuma akan abibda ya shafi fagen addini.
Allah Ta’ala Ya sa al’ummar mu su kara fahimtar irin wadannan lamura na hasken ilimi da cigaban zamani a cikin lamuran rayuwar duniya da addini.
https://www.facebook.com/100003514834672/posts/5731823570278081/?app=fbl
Daga Malam Murtala Isah Dass.