October 6, 2021

Katsina: An hallaka mutane 10 a yayin da suke sallar magriba

Daga Isah Musa Muhammad


Rahotanni da suke zuwa daga jahar Katsina na nuna cewa a kalla mutane 10 ne suka rasa rayukan su a yankin Yasore da ke karamar hukumar Batsari a jahar Katsina bayan shigar yan bindiga gari a jiya Talata.

Rahoton ya bayyana cewa mutanen sun hallaka ne a yayin da yan bindigan suka bude musu wuta lokacin da suke gudanar da sallar Magriba.

An yi jana’izar mutanen da suka rasa rayukan su a safiyar yau, kana wadanda suka ji raunuka kuma an dauke su zuwa asibiti don magani.

Wani rahoto daga mazauna garin sun yi zargin cewa yan bindigan sun shigo garin ne daga sansanin da suke boye na Birnin Gwari dake jahar Kaduna.

‘Yan bindigan dai sun farmaki unguwar ne da yammacin ranar Talata misalin karfe 6:30 inda suka cinna wuta a wasu gidaje na unguwar.

Mazauna unguwar sun nuna cewa matakan da aka dauka kan yan bindigan a kwanakin baya yayi tasiri, saboda sun rage kai farmakin da suka saba yi, sai dai duk da haka manoma na cikin matsi ta yadda ba sa iya girbe amfanin gonar su saboda ayyuka na yan bindigan.

Bayan faruwar lamarin a jiya, wasu daga wadanda suka kubuta sun tsere zuwa shallwatar karamar hukumar Batsari don neman mafaka.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan jahar ya tabbatar da faruwar lamarin. inda yace mutane 10 sun hallaka inda wasu 11 suka jikkata.

Jami’in ya nuna cewa harin da yan bindigan suka kawo martani ne ga ‘Yan sa kai (yan banga), domin a kwanakin da suka gabata yan bangan sun rika zagaya yankin kana kuma suka rika yan bindigan, don haka wannan na iya zama martani ne yan bindigan suka yi ga yan bangan.

Daga karshe ya gargadi yan bangan da gujema maimaita abinda suka aikata to babu shakka zasu yi masa hukuncin irin wadanda suke yi ma yan bindiga.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Katsina: An hallaka mutane 10 a yayin da suke sallar magriba”