Kasashen Yankin Tekun Farisa Sun Yi Allawadai Da Harin Ta’addanci A Iran

Kasashen larabawa na yankin tekun farsi sun yi allawadai da harin ta’addanci da aka kai kan hubbaren sha cheraq a birnin shiraz na kudancin kasar Iran a ranar Lahadin da ta gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar UAE na fada a jiya Litinin kasar bata goyon bayan dukkan al-amari na tashe tashen hankula daga ciki har da harin ta’addancin da aka kai kan hubbaren sha cheraq na birnin Shiraz.
Har’ila yau gwamnatozin kasashen Oma, Qatar, Bahrain da Kuwait duk sun yi allawadai da hare haren na Shiraz.
Akalla mutane 2 ne suka yi shahada sannan wasu 8 suka ji rauni a lokacinda wani dan ta’adda dan kungiyar Daesh ya shiga cikin hubbaren yana harbi kan maiuwa da wabi kan masu ziyara a hubbaren. Amma jami’an tsaro sun kama shi da ransa bayan wani lokaci.
A ranar 22 ga watan Octoban shekara ta 2022 ma wani dan ta’addan na kungiyar Daesh ya kai irin wadan nan hare hare wanda ya kashe mutane 15 daga ciki har da mata da yara.
©voh