April 23, 2023
Kasashen Waje Sun Fara Kwashe Mutanensu A Sudan

Rahotanni daga Sudan na cewa kasashen ketare sun fara kwashe mutanen daga kasar.
Bayanai sun ce kasashe da dama ne suka kimsa ko kuma suka kan kwashe mutanensu a kasar ta Sudan a daidai lokacin da rikicin kasar ke kara kamari.
Har yanzu ba tabbas ko kuma wata alama daga bangarorin dake rikici a kasar na mutunta tsaigaita wutar da sukayi alkawari.
Ko a jiya Asabar an yi ta jin kararakin fashewa da kuma musayar wuta a Khartoum babban binrin kasar.
Kawo yanzu alkalumman wucin gadi da hukumar lafiya ta duniya ta fitar sun nuna cewa mutane 413 ne suka ras arayukansu kan wasu sama da 3,500 suka jikkata a rikicin da aka shiga mako na biyu.