April 12, 2023

Kasashen Larabawa Zasuyi Taro Domin Tattauna Alakarsu Da Siriya

 

Ministoci daga wasu kasashen Larabawa zasuyi wani taro ranar Juma’a a Saudiyya, game da batun kasar Siriya.

Kasar Qatar daya daga cikin kasashen da zasu halarci taron ta sanar da cewar kasashe 9 na Larabawa za su hadu domin tattauna alakarsu da Siriya da zummar kawo karshen wariyar da ake nuna mata.

Taron a cewar ma’aikatar harkokin wajen Qatar zai kunshi kasashe irin su Bahrain da Kuwait da Oman da Saudiyya da kuma UAE.

Baya ga hakan akwai sauran kasashen da ake sa ran su halarci taron da suka hada da Masar da Iraki da Jordan.

Masana na ganin taron bai zo da mamaki ba, ganin yadda Shugaban Syria Bashar al Assad da aka mayar da shi saniyar ware tun bayan barkewar yakin basasar kasarsa a shekarar 2011, ya ziyarci kasashen Hadaddiyyar Daular Larabawa da kuma Oman a watanni 2 da suka gabata, inda ya tattauna da shugabannin kasashen.

Kasar Saudiyya ma a watan jiya ta sanar da cewar ta fara tattaunawa da Siriya da zummar da zummar maido da huldar diflomasiya a tsakanin kasashen biyu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kasashen Larabawa Zasuyi Taro Domin Tattauna Alakarsu Da Siriya”