June 20, 2023

Kasashen Larabawa Sun Yi Allawadai Da Dirar Mikiyan Da HKI Take Yi Kan Garin Jenin Na Yamma Da Kogi Jodan

 

Kungiyar kasashen larabawa ta yi Allah wadai da hare haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ta kai kuma take ci gaba da kaiwa a kan garin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan. Ta kuma yi tir da kissan falasdina da rusa gidajensu da kuma kamasu da take yi a garin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kungiyar tana fadar haka a cibiyarta dake birnin Alkahira na kasar Masar a jiya Litnin. Ta kuma kara da cewa gwamnatin HKI ce da alhakin don marda martanin da Falasdinawa suka yi ko zasu yi saboda keta huruminsu wanda sojojin haramtacciyar kasar suke yi.

Abu Ali mataimakin babban sakataren kungiyar ya kara da cewa abinda sojojin HKI suke aikatawa a Jenin ci gaba ne na take hakkin falasdinawa, aikata laifukan yaki da kuma ta’addanci a kan su.

A na shi bangaren ministan harkokin wajen kasar Masar Sami Shukri ya yi allawadai da hare-haren da sojojin suka kai kan jenin, sannan yay i allawadai da hare-haren da suka kai da jiragen sama a kan garin na Jenin wanda yayi sanadiyyar akalla mutane 4 fararen hula da kuma jikatar wasu 64 daga cikin Falasdinawa a yankin

 

©Hausatv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kasashen Larabawa Sun Yi Allawadai Da Dirar Mikiyan Da HKI Take Yi Kan Garin Jenin Na Yamma Da Kogi Jodan”