January 23, 2023

Kasashen Iran da Najeriya za su fadada alakar kimiyya da fasaha tsakanin su

Kasashen Iran da Najeriya sun samar da wani rukuni da zasu yi aiki hannu-da-hannu don fadada alaka a bangarorin kimiyya da fasaha.
An cimma matsaya na kulla wannan yarjejeniyar ne a yayin wata tattaunawa tsakanin mataimakin ministan kimiyya na kasar Iran Hasham Dadashpour da kuma Jakadan Najeriya a kasar Iran Yakubu Santuraki Suleiman kamar yadda yadda kamfanin dillancin labaran kasar Iran ta wallafa.

Bangarorin biyu sun nuna muhimmancin kimiyya da fasaha kana kuma kasar ta Najeriya na nuna sha’awarta na amfana daga kara ta Iran biyo bayan bunkasarta a bangarorin biyu kamar yadda wakilan Najeriya suka bayyana.
A bangare guda, wakilin Iran ya nuna farin cikin sa kana kuma yace kasashen biyu na da kyakkyawar dama na kyautata hadin kai a bangaren kimiya don taimakon juna.

Kasar Najeriya dai ana kallonta a matsayin daya daga kasashe mafiya muhimmanci a nahiyar Afirka, wannan na daga dalilan da yasa kasar ta Iran ke da burin karfafa alakar kimiya tsakanin ta da Najeriya.

Kasar Iran dai na shirye-shiryen daukar dalibai 250,000 daga kasashen waje, don cimma wannan shirin kasar ta yi shirin tura mutanen ta zuwa ga kasashen waje.
Tuni dai kasar Iran ta samar da cibiyar fasaha a Nairobi da ke kasar Kenya, kana kuma tana da cibiyoyin kasuwanci da sauran bangarori a kasasen Unganda, Tanzania, Kotdebuwa, Ghana, Aljeriya, da kuma kudancin Afirka. Kana kuma tana kokarin sake fadada wadannan cibiyoyi zuwa karshen wannan shekarar a lissafin shekarar Fasha. A bangare guda kuma kasar na kokarin kara kasafin shekara na bangaren kasuwancin da kasashen Afirka zuwa Dalar amurka biliyan 5 zuwa karshen shekarar 2025/2026.

A cikin adadin da aka ambata, ana kyautata zaton kasar Najeriya zata lashe kimanin dala biliyan 2.5.

SHARE:
Labaran Duniya, Labarin CIkin Hotuna 0 Replies to “Kasashen Iran da Najeriya za su fadada alakar kimiyya da fasaha tsakanin su”