April 17, 2023

Kasashen duniya na yin kira da a hanzarta tsagaita wuta a Sudan

Rikicin dake faruwa tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai na RSF, na haifar da damuwa iri-iri daga kasashen duniya, inda kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama, suka yi kira da a hanzarta tsagaita bude wuta

Tuni rikicin da ya barke a safiyar ranar Asabar din da ta gabata, ya yi sanadiyar rayukan a kalla mutane 56, da kuma wasu 595 da suka samu raunuka, kuma har yanzu babu alamun lafawarsa.

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya nuna damuwa matuka game da ci gaba da gumurzun da ake yi tsakanin dakarun sojin Sudan, da na RSF, kamar yadda kakakinsa ya bayyana jiya Lahadi.

Guterres ya yi Allah wadai da kakkausar murya, dangane da rikicin da ya yi sanadiyar mutuwa da jikkatar fararen hula, ciki har da ma’aikatan hukumar samar da abinci ta duniya uku da suka mutu, tare da jikkata wasu biyu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta ce, tana ci gaba da bin diddigin lamarin, tare da nuna matukar damuwa kan al’amuran dake faruwa a Sudan, tana mai kira ga bangarorin siyasa, da fararen hula, da sojoji a kasar, da su samar da hanyar warware rikicin.

Shi ma babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul-Gheit, ya bayyana kaduwarsa tare da yin Allah wadai da fadan da ake yi da makamai, musamman a wannan wata na Ramadan mai alfarma

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kasashen duniya na yin kira da a hanzarta tsagaita wuta a Sudan”