Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Yaba Yarjejeniyar Da Saudiyya Da Iran Suka Cimma

Kasashen duniya sun fara mayar da martani game da yarjejeniyar da kasashen Iran da Saudiyya suka cimma a shiga tsakanin kasar Sin.
Amurka ta ce ta samu labarin cewa Iran da Saudiyya sun dawo da huldar diflomasiyya a ranar Juma’a, amma ta nemi karin bayani daga Saudiyyan, a cewar kakakin kwamitin tsaron kasa na fadar White House.
Gaba daya muna maraba da duk wani yunkuri na kawo karshen yakin Yemen da kuma kwantar da tarzoma a yankin gabas ta tsakiya, inji John Kirby, saidai ya ce yana da shakku game da Iran.
Hadaddiyar Daular Larabawa ma ta yi maraba da yarjejeniyar tare da ” yabawa” rawar da kasar Sin ta taka a shawarwarin.
Ita ma Qatar ta bakin Firaministan kasar kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abderrahman bin Jassim al-Thani ya yi maraba da sanarwar yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhane.
Kazalika Iraki da Oman sun yi maraba da sanarwar maido da huldar da ke tsakanin kasashen biyu Iran da Saudiyya, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya bayyana.
Su ma dai ma’aikatun harkokin wajen kasashen Bahrain da Aljeriya da Turkiyya da Lebanon da kuma Sudan duk sun fitar da sanarwa inda suke maraba da yarjejeniyar.