August 27, 2023

Kasashen dake kewayen tekun Pasifik suna da ikon neman diyya daga gwamnatin Japan kan zubar da ruwan dagwalon nukiliya ruwa cikin teku

A kwanakin baya a jere, kasashen dake kewayen tekun Pasifik sun yi tir da matakin gwamnatin kasar Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliya ta Fukushima cikin teku.

A ganin wadannan kasashe ciki har da tsibirin Marshall wadanda ke fama da mummunar matsalar gurbatar muhalli sanadiyar nukiliya, matakin gwamnatin Japan a wannan karo ya sake sanya su cikin matukar damuwa.

Masanan da abin ya shafa sun yi nuni da cewa, bai kamata kasashen dake kewayen tekun Pasifik su daidaita matsalar da kansu, su dandana mummunan sakamakon da ya biyo bayan matakin gwamnatin Japan ba, suna da ikon neman diyya daga gwamnatin Japan game da wannan batu.

A halin yanzu, akwai yarjejeniyoyi da dama da suka yi bayani game da yadda wata kasa ta zubar da gurbataccen abun nukiliya a cikin teku. Kasar Japan ta daddale yarjejeniyoyin kasa da kasa da dama ciki har da yarjejeniyar kula da tekun da babu wata kasa da ta mallaka. Yanzu dai kasar Japan ta sabawa yarjejeniyoyin, babu shakka za ta dauki alhakinta ta kuma biya diyya ga kasashen dake kewayen tekun Pasifik.

Ban da haka kuma, kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ta taba yanke hukunci ga kasar Canada daga shekarar 1938 zuwa 1941, saboda sinadarin sulfur dioxide da kamfanin sarrafa karafa na Trail na kasar Canada ya fitar ya kawo illa ga jihar Washington ta kasar Amurka, don haka aka bukaci kasar Canada ta biya Amurka diyya. Ana daukar wannan shari’a a matsayin tushen dokokin kasa da kasa, domin biyar alhakin kasa kan gurbatar muhalli a sauran kasashe bisa dokokin kasa da kasa.

Ana iya ganin cewa, kasashen da ke gabar tekun Pasifik na iya yin la’akari da wadannan shari’o’i, da kuma daukar mataki na kimiyya kan tabbatar da illolin da ruwan dagwalon nukiliya ta Fukushima ya haifa musu, su kai kara don neman diyya daga kasar Japan, da kare hakki da muradunsu.

Har kullum gwamnatin kasar Japan tana ikirarin tafiyar da harkokin teku bisa doka, amma yanzu ta gurfanar da kanta a gaban kotu. Za a yanke mata hukunci, kana kasashen dake gefen tekun Pasifik za su samu diyya daga wajenta domin wannan batu.

 

©cri.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kasashen dake kewayen tekun Pasifik suna da ikon neman diyya daga gwamnatin Japan kan zubar da ruwan dagwalon nukiliya ruwa cikin teku”