Kasashen BRICS, Sun Kalubalanci Matakan Tilastawa Da Basu Dace Da Na MDD Ba.

Kasashen kungiyar ciniki ta BRICS, sun kalubalanci matakan tilastawa da suka danganta na gashin kai wadanda basu dace ba da ka’idojin kundin tsarin MDD ba.
A ranar Alhamis ne kasashen BRICS suka bayyana damuwarsu kan yadda ake amfani da matakan wadanda suka bayyana cewa suna haifar da mummunar illa kan kasashe masu tasowa.
A cikin sanarwar Johannesburg ta biyu da aka amince da ita biyo bayan taron kolin BRICS karo na 15 na kwanaki uku, kasashen BRICS sun kuma nanata kudurinsu na inganta da kyautata gudanar harkokin kasa da kasa.
Haka zalika sun sha alwashin sa kaimi kan raya tsarin sassa daban daban na duniya mai dacewa, da dimokiradiyya.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar ta BRICS, ta sanar da amincewa da kasashe shida a matsayin sabbin mambobinta daga ranar 1 ga watan Janairun badi.
Kasashen shida sun hada da Saudiyya, Iran, Habasha, UAE, Masar da kuma Argentina.
©VOH