January 7, 2023

Kasar Turkiyya Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Yaki Da Ta’addanci

Ministan Tsaron Turkiyya ya ce: Ba za su yarda da kasancewar ‘yan ta’adda a kusa da kan iyakokin kasarsu ba

Ministan tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar ya jaddada cewa: Kasarsa ta bayyana matsayinta a yayin zaman taron bangarorin uku da aka yi a birnin Moscow cewa: Turkiyya ba za ta amince da kasancewar wadanda ta bayyana a matsayin ‘yan ta’adda a yankin da ke kusa da iyakar kasarta ba, lamarin da ke nuni da cewa; gwamnatin Turkiyya ba za ta iya daukar nauyin karin wasu ‘yan gudun hijira ba.

Ministan tsaron ya kara da cewa; Gwamnatin Turkiyya ta bayyana matsayinta a fili, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar ta’addanci, sannan ba ta da wata manufa face yaki da ta’addanci, haka nan kamar yadda aka sani akwai ‘yan gudun hijirar Siriya kusan miliyan 4 a cikin kasar Turkiyya, don haka bisa ga yanayi da tsarin kasar a halin yanzu, ba za ta iya jure wa karin sabbin ‘yan gudun hijira ba, saboda haka manufarsu ita ce ‘yan gudun hijirar Siriya su ci gaba da zama a yankunansu.

 

Hausa TV

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kasar Turkiyya Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Yaki Da Ta’addanci”