Kasar Togo Ta Sanar Da Kashe Masu Ikirarin Jihadi Fiye Da 100.

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ne ya bayyana cewa; A wani taho mu gama da aka yi a Arewacin kasar, sojoji kusan 40 sun kwanta dama, yayin da aka kashe masu ikirarin jihadi su 100.
Shugaban kasar ta Togo dai ya bayyana hakan ne a wata hira da ta tashar talabijin ta “ New World Tv” ta yi da shi da a ciki ya ce: Mun sadaukar da kai sosai, musamman jami’an tsaro,domin mun yi rashin 40 daga cikinsu, wanda abin takaici ne. Haka nan kuma mun yi rashin wasu fararen hula da sun kai daruruwa.”
Wannan dai ita ce hira irinta ta farko da shugaban kasar ya yi tun bayan da ya shiga office a 2005 bayan rasuwar mahaifinsa wanda ya dare kan karagar mulki tun wajen 1967.
A cikin wani sashe na hirar tashi, shugaban kasar ta Togo ya gargadi ‘yan kasar da su kwana da sanin cewa yakin da ake yi da ‘yan ta’adda zai iya daukar lokaci mai tsawo. Sai dai ya yi musu alkawalin cewa a karshe gwamnati za ta yi nasara.
Haka nan kuma ya bayyana yadda kusan mutane 12,000 su ka zama ‘yan gudun hijira a cikin kasar.
A wannan shekarar ne dai kasar ta Togo take cika shekaru 63 daga samun ‘yanci daga ‘yan mulkin mallakar Faransa.