June 20, 2023

kasar Sin tana goyon bayan duk wani kokari da zai taimaka wajen warware rikicin kasar Ukraine cikin lumana.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa Talatar nan cewa, kasar Sin tana goyon bayan duk wani kokari da zai taimaka wajen warware rikicin kasar Ukraine cikin lumana.
A kwanakin baya ne, wasu manyan ‘yan siyasa daga kasashen Afirka irin su Afirka ta Kudu, da Senegal, da Zambia, da Comoros, da Masar, da Kongo(Brazzaville), da Uganda, suka ziyarci kasashen Ukraine da Rasha, domin shiga tsakani kan batun kasar Ukraine. Mao Ning ta yi nuni da cewa, kasar Sin ta yaba da rawar da kasashen Afirka suka taka ta wannan fanni.
Ta ce, wannan na nuni da cikakken kiraye-kirayen da gamayyar kasashen duniya ke yi na ganin an tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin, da sassauta halin da ake ciki. Bayanai sun tabbatar da cewa, yaki da takunkumi ba za su magance matsalar ba, kuma tattaunawa ita ce hanya daya tilo da za a iya bi don warware matsalar. Kasar Sin tana son yin aiki tare da dukkan bangarori, ciki har da kasashen Afirka, wajen samar da yanayi mai kyau don warware rikicin kasar Ukraine a siyasance.

 

©Cri (Ibrahim)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “kasar Sin tana goyon bayan duk wani kokari da zai taimaka wajen warware rikicin kasar Ukraine cikin lumana.”