January 7, 2023

Kasar Amurka Ta Gabatar Da Taimakon Kudi Ga Ukraine Saboda Yakinta

Kasar Amurka ta bayyana gabatar da taimakon soji ga Ukraine na dalar Amurka biliyan uku

Gidan talabijin na Aljazeera ya nakalto cewa: Gwamnatin kasar Amurka ta gabatar da tallafin tsaban kudi dalar Amurka biliyan uku ga kasar Ukraine sakamakon yakin da take yi da kasar Rasha, kamar yadda kasashen Jamus da Faransa suka ba da sanarwar taimakon soji da suka hada da motocin yaki da na jiragen yaki ga kasar ta Ukraine.

A nata bangaren kasar Rasha duk da sanarwar da fitar na dakatar da bude wuta na bangaren guda kan kasar Ukraine a ranar Alhamis, amma a jiya Juma’a an samu bullar ci gaba da musayar wuta tsakanin bangarorin biyu kafin sanar da shirin dakatar da bude wutar da kuma bayansa. Kakakin ma’aikatar tsaron Rasha Igor Konashenkov ya ce: Sojojin Ukraine sun ci gaba da kai hare-hare kan gidajen fararen hula da kuma sansanonin sojin Rasha, duk kuwa da matakin dakatar da bude wuta da bangaren kasar Rasha ya dauka.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kasar Amurka Ta Gabatar Da Taimakon Kudi Ga Ukraine Saboda Yakinta”