June 21, 2023

Karuwar Tashe-tashen Hankula A Gabar Yammacin Kogin Jordan

An kashe wasu ‘yan Isra’ila hudu a wani harin bindiga na daukan fansa da falasdinwa suka kai a kusa da wani kauye da ke Yamma da gabar kogin Jordan da ke karkashin mamayen Isra’ila, wanda ya kara fiddo da zaman dar-dar a yankin sakamakon matakan tsokana da Isra’ila ke dauka.

Lamarin dai ya zo ne bayan karuwar tashe-tashen hankula a Gabar Yamma da Kogin Jordan cikin ‘yan kwanakin nan.

Mai magana da yawun kungiyar Hamas ya ce harin, wani martani ne ga farmakin da sojojin Isra’ila suka kai a Jenin ranar Litinin da ta gabata, inda Falasdinawa shida suka mutu.

Mai magana da yawun rundunar tsaron Isra’ila Rear Admiral Daniel Hagari ya fada a cikin wata sanarwa cewa ‘yan bindigan sun bude wuta a wani gidan cin abinci na hummus da ke gefen hanya, inda suka kashe fararen hula uku, sannan suka harbe wani farar hula a gaban wani gidan

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Karuwar Tashe-tashen Hankula A Gabar Yammacin Kogin Jordan”