October 1, 2021

Kano: Gobara a gidan Talabijin na “ARTV”

Daga Bala Ishaka


An samu tashin gobara a gidan talabijin na Abubakar Rimi wato “ARtv” wanda ya kasance mallakin gwamnatin jaha.

 

Ya zuwa yanzu babu masaniya kan abin da ya sabbaba tashin gobarar. Rahotanni sun nuna cewa jim kadan bayan tashin gobarar yan kwana-kwana suka hallara kana kuma suka yi iya bakin kokarin su don kashe gobarar domin kubuce ma asarar rayuka da dukiya.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kano: Gobara a gidan Talabijin na “ARTV””