October 11, 2021

Kano: An sauke Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai

Daga Mudassir Al’amin


Majalisar malamai ta jahar Kano ta sanar da dakatar da shugaban ta Sheikh Ibrahim Khalil daga mukamin sa a yau Litinin.

Tuni dai bayan dakatar da shi din aka sanar da maye gurbin sa da Sheikh Abdullahi Sale Pakistan.

Majalisar ta sanar da dalilan ta na dakatar da malamin, inda daga ciki ta bayyana cewa malamin na kokarin siyasantar da majalisar malaman, kana a bangare guda kuma yake amfani da ita don biyan bukatun kashin-kai wanda hakan kuma ya saba da dukkan sharruda da ka’idojin majalisar.

Wasu gungun malamai daga bangarori uku da suka hada da Tijjaniyya, Kadiriyya da kuma izala sun nuna goyon bayan su da kuma cimma matsaya guda kan lamarin.

Kafin nadin Sheikh Pakistan matsayin shugaban majilisan malaman, malamin dai ya kasance shugaban kungiyar Izala ta jihar Kano.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kano: An sauke Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai”