June 2, 2023
Kano: An haramta mana fasta da talluka a gine-gine a fadin jihar

Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya haramta manna Fasta da talluka a gine-ginen da ke jihar.
Gwamnan ya ce za a samar da kwamitin da zai tabbatar an bi wannan mataki domin daina ɓata kadarorin Gwamnati dana jama’a.
Ya shawarci masu tallace-tallace da su yi amfani da allunan talla na zamani masu amfani da lantarki.