February 27, 2023

Kano: Alhassan Doguwa ya sake lashe zaben dan majalisa a karo na 6

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya sake lashe kujerarsa a karo na shida.

Alhassan, wanda ke waliktar mazabar Doguwa da Tudun Wada daga jihar Kano ta kashe zaben ne da kuri’a 39,732, inda ta doke abokin hamayyarsa na kurkusa, Yushau Salisu Abdullahi na jam’iyyar NNPP, wanda ya sami kuri’a 34,798.

Dan takarar jam’iyar PDP kuwa, Jamilu Dayyabu, ya sami kuri’a 2,091 ne.

Daga Clement A. Oloyede da Sani Ibrahim Paki

Doguwa dai ya fara zuwa Majalisar Wakilai ne shekarar 1992 sannan ya sake komawa a shekara ta 2007.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kano: Alhassan Doguwa ya sake lashe zaben dan majalisa a karo na 6”