March 12, 2023

​Kanaani: Kyautata Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Zai Kawo Manyan Sauye-Sauye A Yankin.

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naser Kanaani ya bayyana cewa, kyautata alaka tsakanin Iran da saudiyya zai kawo manyan sauye-sauye a yankin gabas ta tsakiya.

Kanaani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan rattaba hannu karyeyeniyar maida alaka tsakanin Iran da Saudiyya da aka rattaba hannu a kanta a jiya Juma’a a kasar China.

Ya ce: kasashen Iran da Saudiyya su ne kasashe mafi girma a yankin gabas ta tsakiya, kuma makwabtan juna masu tsohon tarihi, kamar yadda kuma su ne manyan kasashen musulmi biyu mafi tasiri a duniya, wanda hakan zai taimaka wajen warware matsaloli da dama na yankin.

Ya kara da cewa, kasashen yammacin turai sun yi iyakacin kokarinsu domin kawo baraka tsakanin manyan kasashen musulmi biyu wato Iran da Saudiyya, amma wanann mataki da kasashen biyu suka dauka, ya rusa shirin kasashen yammacin turai.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Kanaani: Kyautata Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Zai Kawo Manyan Sauye-Sauye A Yankin.”