December 23, 2023

Kamfanin gine-gine na kasar Sin CGC zai gina gadojin kasa biyu a jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta bayar da kwangilar naira biliyan 15.97 ga kamfanin China Geo-engineering Corporation CGC domin gudanar da aikin ginin gadojin kasa a cikin birnin Kano.

Kwamashinan yada labarai na jihar Baba Halilu Dantiye ne ya tabbatar da hakan jiya Juma’a 22 ga wata lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa. Ya ce, aikin ginin gadojin za a gudanar da su ne a shatale-talen unguwar Dan-Agundi da kuma na Tal’udu.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kamfanin gine-gine na kasar Sin CGC zai gina gadojin kasa biyu a jihar Kano”