July 28, 2021

KALUBALEN DA MASU NOMAN SHINKAFA SUKE FUSKANTA.

KALUBALEN DA MASU NOMAN SHINKAFA SUKE FUSKANTA.

 

Shinkafa ta kasance daya daga abincin mafiya yawan Al’ummar Duniya ta dogara dashi a matsayin abinci, to amma duk da kokarin nomata tare da wasu kayan abinci da ake yi a Najeriya har yanzu kasar ba ta iya samar da adadin shinkafar da za ta dogara a kai.

Binciken hanyoyin da za’a bi domin bunkasa noman shinkafa da kuma sarrafa ta shine abinda ya kamata hukumomi su maida hankali a kai. A binciken da jaridar Ahlul baiti ta gudanar ta hanyar amfani da wasu alkaluma da rahoto da kafar sadarwa ta BBC Hausa tayi cewa ” jihar Kano da ta yi fice a noman shinkafa tun shekaru aru aru.

Salisu Kura, wani manomi a garin kura dake jihar ta Kano ya shaida mana cewar,  yawancin mutane sun fi siyan shinkafar waje saboda ta fi haske, ya ce;” A gani na ina ganin ta Hausa ta fi dadi da kuma aminci domin bamu san illar da ke tattare da shinkafar kasar waje ba”.

“Muna fuskantar matsalar samun isashen takin zamani saboda, takin da gwamnati ke rabawa ba ya kaiwa ga manoma, kuma idan mun noma masu kudi suke zuwa su siya da araha kuma su sake dawowa da shi kasuwa domin siyarwa da tsada”. In ji Salisu Kura.

Mai gwamnati ke yi?

Bayanai dai sun sha nuna cewa,gwamnatoci na da babban aiki wajen tallafawa domin inganta samar da abinci. kuma ko wacce irin rawa gwamnati ke takawa ta tallafawa manoma kamar Salisu?

Wani jami’in yada labarai na jihar Kano,ya shaida mana cewa gwamnatinsu na tallafawa manoma ta hanyoyi da dama.

“Gwamnati ta samarwa matasa manoma a jihar takin zamani mai rahusa domin taimaka musu; mun kuma samar da hanyoyin zamani na inganta noman shinkafa inda za a samarda iri dabam dabam wanda zai taimaka wajen samar da shinkafi mai yawa”. In ji Jami’in.

A takaice dai kamar yadda yake kumshe a rahoton, Jaridar Ahlulbaiti ta fahimci cewa “babbar matsalar da ke fuskantar manoman shinkafar dai, ita ce ta rashin injina na zamani wadanda zasu taimaka wajen noman shinkafar da yawan gaske,da kuma sarrafata ta inda za ta yi kankankan da ta kasashen ketare.

 

Daga

Ahmad Ahmad

 

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “KALUBALEN DA MASU NOMAN SHINKAFA SUKE FUSKANTA.”