February 14, 2023

Ka’idojin yadda ake kai tsofaffin takardun kudi a babban bankin CBN

1. Idan ka kai kudin ba za a chanza maka da sababbi ba, sai dai a saka maka acikin asusun ajiyarka na banki (Account)

2. Hukuma zata bincika ta tabbatar da cewa asusun ajiyarka baya da wata matsala, kamin asaka maka kudin, idan aka fahimci akwai damuwa ga asusunka na banki, to za a dawo maka da kudinka.

3. Wani ba zai kai kudin wani ba. Kowa shi zai kai kudinsa da kansa kuma asusun ajiyarsa na banki zai bayar a saka kudin aciki.

4. Kamin ka tafi bankin CBN domin kai kudi, akwai bukatar ka ziyarci shafin yanar gizo na bankin domin cike form na saka kudin, domin ka samu reference number da zaka yi amfani da ita. (Wanda ya kasa yin wannan, za a bashi form din ya cike a can)

5. Wanna aiki za a gudanar da shi daga nan zuwa 17 February (wato 17 ga wannan wata da muke ciki) kuma zai a rufe daga wannan lokaci.

Abubakar Sadiq, Gusau

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ka’idojin yadda ake kai tsofaffin takardun kudi a babban bankin CBN”