August 28, 2023

KA’IDA TA FARKO MECE CE NASARA?

Kowane mutum a wannan rayuwar yana son ya yi nasara ya samu farin ciki, yana burin ya samu nasara a rayuwarsa. Sai dai mene ne shi? Kuma a ina za mu same shi?
Wasu suna ganin farin ciki yana tattare da tara dukiya, sai dai shin mawadata sun yi nasara kuma suna cikin farin ciki?
Wasu kuma suna ganin nasara tana tattare da yin kyau; Yayin da Wasu kuma suna ganin nasara tana tattare da samun sheda ta takardun samun ilimi da sauransu.
Sai dai wadannan lamura dukkansu suna yin nuni ne da wani gefe daga cikin nasara ko farin ciki, ba su ne nasara ta hakika ta har abada ba.
Lallai yin imani da Allah da jin tsoronsa ita ce daidaitacciyar hanyar isa ga samun nasara ta duniya da ta lahira. Kuma wannan ita ce hanya dodar da take bayyanar da mutumtakarsa, saboda imani yana dasa nutsuwa a cikin zuciyar mutum, ya sami daidaito da kwanciyar hankali, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake fada a cikin suratur Ra’ad: 28:
(الَّذِينَ آمَنُواْ وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ اللّهِ أَلاَ بِذِكْرِ اللّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ).
Ma’ana: Wadanda suka yi imani zukatansu suka nutsu da ambaton Allah, ku saurara da ambaton Allah ne zukata suke samun nutsuwa.
Shi kuma barin ambaton Allah yana haifar da tsiya da kincin rayuwa da rashin tabbas da damuwa da cututtukan zuciya. Allah madaukakin sarki yana fada a cikin suratu Daha: 124:
(وَمَنْ أَعْرَضَ عَن ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنكًا وَنَحْشُرُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَعْمَى).
Ma’ana: Duk wanda ya bar ambatona, to zai yi rayuwa ta kunci, mu kuma tashe shi a makaho ranar Alkiyama.
Lokacin da imani ya shigi mutum, ya karfafa a jikinsa, hakan yana mayar da shi ya zama madaukaki.
A lokacin da imani yake karuwa ga mutum duk wata baiwa da yake da ita tana karuwa, kamar: Karfin ikonsa da tabbatuwarsa da nutsuwarsa da son aiki da karfin akida da sabawa da kyauta da sauransu.
Dukkan wadannan manyan ginshikai ne da suke sanya mutum zama madaukaki, kuma sun kasance matattakala da zai hau zuwa ga samun nasara da farin ciki.
Shi imani ilimi ne da aiki, ba nazari kawai ba ne, zai kasance a zuci gabobi kuma su bayyana shi a aikace. Akwai kakkarfar alaka tsakanin imani da aiki, a nan ne za mu fahimci rawar da imani yake takawa wajen riskar da mumini zuwa ga kololuwar nasara da rabauta.

 

©✍🏽 Mujtaba Shu’aibu Adamu

SHARE:
Makala 0 Replies to “KA’IDA TA FARKO MECE CE NASARA?”