August 14, 2021

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 8

Muhammad Bakir Muhammad

Rahoto dake fitowa daga jihar Kaduna ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe kalla manoma a kalla 8 a kauyukan Buruku da Udawa.

Kauyukan dai guda biyu suna karkashin karamar hukumar Chikun na garin Kaduna kuma sun kasance a tsakankanin yankin babban titin Birnin Gwari.

Rahoton dai ya nuna cewa manoman an farmake su ne a yayin da suke tsaka da aiki a gonakan su.

A kalla manoma 5 aka kashe a kauyen Buruku mutum 3 kuma a garin Udawa duka a karamar hukumar ta Chikun, kauyukan dai suna yawan fiskantar irinwadannan matsaloli na ‘yan bindiga da kuma kisan manoma.

Mutanen kauyukan sun koka inda suka bayyanawa manema labarai cewa sun gaji da bisne mutanen su; wadan da suka rasa rayukan su sanadin harin na ‘yan bindiga kana kuma sun nuna bukatar taimako daga hukuma.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 8”