October 30, 2021

Kaduna: Jami’an tsaro sun hallaka ‘yan bindiga da dama kana kuma sun cafke shugaban su

Daga Isah Musa Muhammad


Jami’an tsaron Nijeriya sun hallaka ‘yan bindiga da dama inda suka kone sansanin su a yayin gudanar da “atisayen shara” wanda ya gudana a kananan hukumomin Igabi da Chikun duk a jihar Kaduna.

Bugu da kari, jami’an sun cafke shugaban yan bindiga na yankin, wanda ake kira Malam Idris Audu, a tare da shi kuwa sun damke wata mata mai suna Rabi Hajiya Karime wacce ta kasance mai dakin wani sanannen dan bindiga mai suna Zubairu.

Kwamsihinan harkokin tsaro na cikin gida a jihar Kaduna, Samuel Aruwan shine ya bayyana hakan a jiya Juma’a.

Ya kuma kara da cewa sun cafke wasu da ake zargi na hulda da yan bindigan, mutanen da aka damke din sun hada da Abdurrashid Gambo Na-Halima da kuma Abubakar Idriss Na-Halima.

Kwamishina Aruwan ya bayyana cewa an gudanar da atisayen ne a wuraren da suka hada da Barebari, Katuka, Maguzawa da kuma Faka.

Ya kuma kara da cewa jami’an tsaron sun gudanar da kamen masu laifuka zuwa Katuka wanda ta kasance kimanin kilomita 9 daga yankin Kangon Kadi dake karamar hukumar Chikun.

Daga karshe kwamishinan ya shaida wa manema labarai cewa sun samu ganimar wasu babura da kuma wasu makaman AK47 da harsasai kana kuma a bangare guda sun samu muggan kwayoyi na maye wadanda suka kasance mallakin yan bindigan a sansanin su dake Udawa duk a karamar hukumar Chikun.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kaduna: Jami’an tsaro sun hallaka ‘yan bindiga da dama kana kuma sun cafke shugaban su”