January 13, 2024

Bakiru Da Ya Tare Ilimin Annabawa.

Kuzo Kuji Kaɗan Daga GirmanSa

Wancan da Allah yake yi masa sallama yake gaishe shi “Ina nufin Annabi Muhammad (S)”

Dukka taron Annabawa ma suna yi masa sallama kuma suna gaishe shi.

Shine yace: Ya Jabir wajibi ne kai kayi tsawon rai, domin ka isar da saƙon sallama na da gaisuwa ta ga Bakiru wanda ya tare ilimin dukkanin Annabawa.

Shi yasa nake cewa: “Rayuwar Sahabi Jabir da tayi tsawo albarkacin Addu’ar da Annabi yayi ne domin isar da wannan sallama faƙat.

Sunansa Muhammad amma sai akayi masa laƙabi da Baƙir.

Wannan laƙabi wanda ya zaɓa masa ita shine: wanda baya magana da son ransa, sai dai idan wahayi akayi masa.

An samu ittifaki Sunnah da Shi’a cewa: laƙabin Baƙir an yi ta ne a jikan Annabi wanda shine Muhammad bin Ali.

Sannan shi shugaba da kansa ya fassara wannan suna.

Baƙir, Meyasa Baƙir?

Domin shi yana faɗaɗa ilimin Annabawa faɗaɗawa.

– Fassarar Jawabin Shugaban Hauzozi Ayatullah Sheikh Wahid Kurasani (DZ).

– Mai Fassara: Amjad Mukhtar Imam.

13/01/2024,

Amjad Mukhtar Imam

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “Bakiru Da Ya Tare Ilimin Annabawa.”