September 28, 2021

Jirgin Yaki Yayi Luguden Wuta Kan Masu “Su” A Borno

Daga Isah Musa Muhammad


An kiyasta cewa a kalla mutane 20 ne suka rasa rayukan su sakamakon luguden wuta da rundunar sojin Najeriya ta yi a wani yanki da ake zargin cewa mafaka ne na yan ta da kayar baya a jahar Borno.

A safiyar Lahadi ne jirgin yayi luguden wuta a Kwatar Daban Masara da ke yankin tafkin Chadi.

A yan kwanakin baya ne rahotanni suka fita kan rasa rayuka da kuma jikkata da wasu suka yi a wasu kauyukan Arewa ta gabashin Najeriya sakamakon luguden wuta da wasu jiragen yaki suka yi.

A wannan karon wasu jami’ai da mutanen da ke makobtaka da garin sun nuna cewa manufar harin shine a farmaki yan ta’adda da ke yankin amma kuma anyi rashin sa’a inda harin ya ritsa da wasu fararen hula da suke a wurin don kamun kifi.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Jirgin Yaki Yayi Luguden Wuta Kan Masu “Su” A Borno”