May 19, 2024

Jirgin Sama Dauke Da Shugaban Kasar Iran Da Tawagarsa Ya Yi Hatsarin A Lardin Azarbaijan Ta Gabas

Labaran da ba’a tabbatar ba sun bayyana cewa jirgin sama dauke da shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da tawagarsa ya fadi a yankin Jalfa da ke cikin lardin Azerbaina na arewa maso yammacin kasar a dazo dazon nan.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya bayyana cewa jami’an agaji na Hilal Ahmar da sauran wadanda abin ya shafa suna kokarin gano inda jirgin shugaban kasar ya fadi a cikin tsaunuka a yankin, kuma yanayi a yankin bai da kyau sosai, saboda ruwan sama da kuma yayyafin da ake yi.

Ministan cikin gida Ahmad Wahidi ya fadawa tashar talabijin ta labarai ta kasa IRINNA kan cewa an tura jiragen ‘drone’ zuwa kan tsaunukan da hatsarin ya auku don gano inda jirgin ya fadi.

Ministan ya kara da cewa shugaban da tawagarsa sun dauki jiragen sama masu saukar angulu a tafiyar tasu ta zuwa da dawowa.

Amma daya daga cikin jiragen yayi saukar gaggawa saboda bacin yanayi. A halin yanzu dai ma’aikatan agaji suna kokarin gano inda jirgin ya fadi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Jirgin Sama Dauke Da Shugaban Kasar Iran Da Tawagarsa Ya Yi Hatsarin A Lardin Azarbaijan Ta Gabas”