April 17, 2023

​Jirgin Ruwan Yaki Na Amurka Ya Ratsa Ta Mashigar Ruwan Taiwan Na Kasar Cana A Jiya Lahadi

Jirgin ruwan yaki na Amurka USS Milius ya ratsa ta mashigar ruwa ta Taiwan wanda ya raba tsibirin da babban kasa ta Cana, sannan ta bada sanarwan cewa yi haka ne a shirinta na yin hakan kamar yadda ta saba.

Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP ya bayyana cewa a ranar litinin da ta gabata ce sojojin ruwa na kasar Cana suka kammala rawar daje a cikin mashigar ta Taiwan, inda ta gwada yiyuwar toshe mashigar da kuma yi wa Taiwan kawanya da kuma kwace iko da tsibirin.

Gwamnatin kasar Cana ta gudanar da rawar daji a matsigar ruwan ne bayan da shugaban tsibirin Taiwan ya gana da kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Kevin McCarthy a tsibirin.

A karkashin shirin “Cana Guda” dai kusan dukkan kasashen duniya sun amince da cewa tsibirin Taiwan bangare ne na kasar Cana. Daga cikin har da gwamnatin kasar Amurka kanta don bata da huldar jakadanci da kasar ta Taiwan. Amma duk da haka Amurka taci gaba da goyon bayan tsibirin ta Taiwan da makamai da kuma kudade don ci gaba da takurawa kasar ta Cana.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Jirgin Ruwan Yaki Na Amurka Ya Ratsa Ta Mashigar Ruwan Taiwan Na Kasar Cana A Jiya Lahadi”