January 3, 2023

Jihar Kwara: Jami’an sojan sama biyu sun rasa rayukan su sakamakon wani hadarin Mota

 

Rahotanni daga jihar Kwara na bayyana cewa wasu jami’ai biyu na hukumar sojin Sama sun rasa rayukan su biyo bayan wata hadari da ta auka da su a bakin aiki.

Hadarin dai ya faru ne a yayin da wata motar Tirela ta murkushe jami’an biyu har lahira a sabili da shanyewar birkin motar.

 

Lamarin dai ya auku ne a gadar Pasa dake yankin Eyenkorin wanda ya kasance babu tazara sosai tsakanin sa da mazaunar jami’an sojan sama. Faruwar lamarin ya haifar da tashin hankali ga mazauna yankin da kuma unguwannin da ke kewaye da wajen.

Tuni dai aka tsaurara ratso a wajen biyo bayan faruwar lamarin. Shaidar gani da ido daga mazauna unguwar sun shaida cewa jami’an sun kasance a bakin aiki a yayi da Tirelar ta tunkare su inda daga baya tayi ajalin su.

 

Matukin motar ya yi kokarin tserewa biyo bayan faruwar lamarin, sai dai kuma daya daga cikin jami’ai ya harbe shi a kafa inda ya kama shi.

Tuni dai mazauna yankin sun nuna damuwar su kana kuma sun nuna bukatar dauke sansanin jami’an sojan saman daga unguwar tasu zuwa wani wajen na daban.

 

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan jihar Kwara da kuma Kwamandan hukumar kawo agajin gaggawa sun sanar da faruwar al’amarin

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Jihar Kwara: Jami’an sojan sama biyu sun rasa rayukan su sakamakon wani hadarin Mota”