August 12, 2021

Jihar Kebbi: Annobar Kwalara Ta Kashe Mutum Sama Da Dari

Muhammad Bakir Muhammad

Sakamakon ballewar cutar kwalara a jihar ta Kebbi a kalla mutune wadanda adadin su bai gaza 140 ba sun rasa rayukan su.

Duk da cewa bamu samu cikakken rahoto kan lokacin da mutuwar ya wakana ba, amma mun samu tabbacin cewa cutar ta yadu a dayawa daga kananan hukumomin jihar wanda a kalla sun kai kananan hukumomi 20.

Wata majiya ta tabbatar da cewa mutane wanda kimanin su ya kai 2,208 sun kamu da cutar bayan gwajin da aka yi musu a yan kwanakin nan.

Sai dai kuma hukumomin kiwon lafiya a jihar sun tabbatar da suna bakin kokarin su wajen tabbatar da yaki da annobar, sannan suna kan aikin wayar da kan al’umma kan ka’idoji da zasu rika bi don gujema kamuwa da cutar ta kwalara.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Jihar Kebbi: Annobar Kwalara Ta Kashe Mutum Sama Da Dari”