October 10, 2021

Jigawa: ‘Yan sanda sun damke ‘bata-gari 14

Daga Mustafa Gumel


Hukumar yan sandan jahar Jigawa ta bayyana cewa ta samu nasarar damke wasu bata gari guda 14 a kananan hukumomin Gumel da Kazaure duk a jihar Jigawa.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jahar, ASP Lawan Shiisu ne ya tabbatar da faruwar hakan ga kamfanin dillancin labarai ta Nijeriya (NAN).

Jami’in ya bayyana cewa sun kai samamen ne kan sansani da kuma daba wanda ‘bata gari ke buya inda kuma suka yi nasarar kama masu laifuka har mutane 14.

Yayin samamen jami’an yan sandan sun kama wasu kayayyaki da suka hada da ganyen wiwi, wasu babura guda 2 marasa rajista, da sauran su.

Jami’in kuma ya bayyana sakon kwamishinan yan sanda Aliyu Sale inda yake shawartar bata-garin da su kauracewa aikata laifuka da kuma biyayya ga doka da oda ko kuma su bar jihar. Ya bayyana cewa rashin daukan daya daga cikin wadannan biyu ka iya haifar da mummunan hukunci kan duk wanda suka kama.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Jigawa: ‘Yan sanda sun damke ‘bata-gari 14”