November 21, 2022

JAWABIN BAYAN TARON MAULUDIN KHATMA NA Mu’assasar Rasulul A’azam (RAAF) Asabar 24 Rabi’us Sani, 1444 / 19 Nuwanmba, 2022

 

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai.

Wannan Kungiya tana godiya wa Allah Maɗaukaki da Ya kawo mu kammala tarukan Mauludin shekara ta
2022 cikin nasara. Allah Ya maimaita mana, Ya karawa Annanbi (SAWA) daraja da daukaka.
Muna mika godiya ga duk waɗanda suka yi tsayin-daka wajen tabbatuwar wannan nasara, daga shugabanni na siyasa da
Sarakuna, da Jami’an tsaro, wadanda suka tabbatar da tsaro da amincin mahalarta tarurrukan mu na
mauludi a fadin kasar nan.
Bayan haka, kamar yadda al’adar wannan kungiya ta saba, muna gabatar da
kiraye-kiraye masu zuwa:

1- A daidai lokacin da guguwar siyasa ta fara kaɗawa a fadin kasar nan, muna kira ga a al’ummar
Nijeriya da ta shirya wa zaɓuɓɓukan shekara ta 2023 masu zuwa cikin lumana da zabin shugabanni na masu rikon amana da kula da haƙƙoƙin jama’a da walwalarsu.

2- Muna kira ga ‘yan takarkaru da masu tallata su da su guji kazantar siyasa na miyagun maganganu da
ayyukan ash-sha ga junansu da sauran al’umma baki daya.

3- Muna kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi da jajircewa wajen fuskantar
matsalolin tsaro da ake fuskanta a sassa daban daban na ƙasar nan, musamman matsalolin garkuwa da mutane da ya addabi wasu sassa na Kasar nan.

4- A nan muke bayar da shawara da kara shigar da masu mukaman sarautun gargajiya don samun
nasarar shawo wannan matsala, masamman a arewacin Nijeriya.

5- Bisa girmamawa ga sarakunan mu masu martaba muke fatan ganin sun shiga gaba wajen magance matsalolin mu na cikin-gida, musamman a tsakanin Musulmi.

6- A daidai wannan lokaci kuma, muna kira ga jama’a da su guji siyasantar da harkokin tsaro da daukar
lamarin sakwa-sakwa.

7- Muna kira ga gwamanatin tarayya da na jihohi da su kara daukan matakan saukaka wa talakawan ƙasar nan halin matsin rayuwa da suke fuskanta a sababin tabarbarewar tattalin arzikin duniya da
harkokin cin-hanci da rashawa da wasu marasa kishin kasa suke tafkawa.

8- Muna kira ga Kungiyar malaman Jami ‘a (ASSU) da gwamanatin tarayya da kaucewa sake jefa
ɗaliban jami’a cikin halin rashin tabbas wanda yajin aikin malaman Jami’a ke haifarwa.

9- Muna kara jaddada kira ga matasa da su guiji fadawa harkokin bangar siyasa, shaye-shayen muyagun kwayoyi da daba, don samun zarafin gina kansu a ilimi da tattalin arziki da cl-gaba a rayuwa.

10- Muna jaddada kira zuwa ga mambobin wannan kungiya ta mu da rungumar hada-hadar ilimi da sana’u tare da taimakon kai-da-kai da bayar da gudunmawa wajen gina ƙasa da tabbatar da zaman
lafiya.

11- Muna kara kira ga al’ummar Musulmi da su rungumi karantarwar Musulunci na haɗin-kai, da gujewa tsaurin-ra ayi da kausasan wa’azozi da yaɗa ƙyamatar da juna.

12- Muna kira da babbar murya na rungumar hanyoyin lumana da bin dokoki wajen neman hakkoki, gami da gujewa duk abin da ke iya kawo tashin hankali da rikice rikice.

Allah Ya kare mu da kasar mu baki ɗaya.

Bissalam.

Sheikh Saleh Muhammad Sani Zariya❤️🌹
Babban Sakatare
19/11/2022

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “JAWABIN BAYAN TARON MAULUDIN KHATMA NA Mu’assasar Rasulul A’azam (RAAF) Asabar 24 Rabi’us Sani, 1444 / 19 Nuwanmba, 2022”