Jam’iyyar ANC Mai Mulki A Kasar Afirka Ta Kudu Na Son Kasar Ta Fice Daga Kotun Duniya Ta Manyan Laifuka

Shugaban kasar ta Afirka Cyril Ramaphosa ya fadi cewa; Jam’iyyarsa ta ANC tana son ganin an fitar da kasar daga cikin yarjejeniyar da ta kafa kotun duniya ta manya laifuka.
Ramaphosa ya kuma ce; Matsayar jam’iyyar ta ANC akan batun ficewa daga kotun duniyar ya biyo bayan sukar da ake yi wa kasar ne saboda mahangarta akan yakin Ukiraniya.
Kotun ta manyan laifukan ta kasa da kasa ta fitar da sammacin a kamo mata shugaban kasar Rasha Vladmir Puti saboda zarginsa da ake yi da aikata laifukan yaki a kasar Ukiraniya.
A cikin watan Ogusta ne dai kasar Afirka ta kudu za ta karbi bakuncin kungiyar nan ta BRICS, wacce ta hada ita kanta mai masaukin bakin, Brazil, China India da kuma Rasha.
Kotun ta duniya za ta so ganin gwamnatin Afirka ta Kudu ta kame shugaban kasar ta Rasha, idan ya sauka a kasar, ta kuma mika ma ta shi.