January 15, 2023

Jama’a suna ci gaba da zanga-zanga a fadin kasar Peru tare da jaddada yin kira ga shugabar kasar kan yin murabus

Rahotonni sun bayyana cewa: Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a ranar Alhamis a kan titunan birnin Lima fadar mulkin kasar Peru, a wani mataki na gangamin lumana domin ci gaba da nuna adawa da sabuwar gwamnati da shugabar kasar Dina Boluarte ta kafa, bayan shafe makwanni ana gwabza kazamin fada da ya barke bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Pedro Castillo, inda ya haifar da hasarar rayukan mutane akalla 42.

Rahotonni sun bayyana cewa: Jama’a suna ci gaba da zanga-zangar a manyan biranen kasar Peru, inda a ranar Alhamis suka fito a birane 10 daga cikin 25 na kasar, ciki har da babban birnin kasar Lima, suna kira ga sabuwar shugabar kasar kan ta yi murabus. Rikicin dai ya kunno kai ne tun a farkon watan Disamba, kuma shi ne tashin hankali mafi muni a kasar ta Peru cikin sama da shekaru 20 da suka gabata.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Jama’a suna ci gaba da zanga-zanga a fadin kasar Peru tare da jaddada yin kira ga shugabar kasar kan yin murabus”