September 7, 2021

Jahar Neja Ta Rufe Bankuna 8 Kan Biyan Haraji

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Hukumar haraji ta jahar Neja ta rufe rassan wasu bankuna da suka kai 8 kan rashin biyan haraji wanda adadin su ya taru yakai sama da naira miliyan dari hudu da Hamsin.

Shugaban hukumar, Mohammed Madami Etsu ne ya bayyana hakan a jiya Litini a garin Minna; Babban burnin jahar.

Kana kuma ya kara da cewa hukuncin ya faru ne bisa tanadadden doka wanda yake tafiyar da hukumar.

Shugaban ya kuma bayyana cawa hukumar su tayi bakin kokarinta wurin baiwa bankunan dama kan ganin sun biya bashin amma kuma bankunan basu cika alkawurran su ba akan lokaci har wa’adin ya cika.


Daga karshe yayi kira ga sauran ma’aikatun da ake binsu bashi da su hanzarta biya akan lokaci don gudun abinda ya sami wadannan bankunan suma ya same su.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Jahar Neja Ta Rufe Bankuna 8 Kan Biyan Haraji”