September 27, 2021

Jahar Kogi: An Sake Damke Fursunonin Da Suka Tsere Daga Gidan Gyaran-Hali

Daga Balarabe Idriss


A yau Litinin ne Gwamnatin jahar Kogi ta tabbatar da sake damke wasu fursunoni 132 da suka tsere daga gidan gyaran hali a garin Kabba.

Kana kuma an bayyana cewa daya daga cikin fursunonin an kama shi a ranar Lahadi yayin da yake kokarin lalata cibiyar lantarki mallakin kamfanin raba wutar lantarki na Abuja.

Mai bada shawara kan harkokin tsaro na jahar kwamanda Jerry Omodara, ya bayyana cewa fusrsunan an kama shi ne a yayin da yake kan lalata taransifoma a yammacin ranar Lahadi, jami’in ya bayyana cewa jahar ta sauya salon dakile matsalolin tsaro a yankin.

Gidan gyaran halin dai an farmake shi ne a kusan makonni uku da suka gabata, inda wasu yan daban haya wadanda ba’a san ko su waye ba suka kutsa ciki kana kuma suka saki fusrsunoni sama da 200 kana kuma suka hallaka wasu daga masu kula da gidan.

A cikin bayanin sa ya bayyana cewa sanyawar idon da gwamnatin ke yi da kuma samar da kayan aiki na musamman kan kawo karshen ta’addanci a jahar bazai canza ba, duk don tabbatar da zaman lafiya da kiyaye lafiyar al’ummar jahar.

Ya kara da cewa, daga faruwar lamarin zuwa yanzu sun yi nasarar dawo da fursunoni 132 zuwa gidan gyaran halin duk a kokarin su na ganin sun samar da zaman lafiya a jahar, kuma ya bayyana cewa zasu cigaba da sabunta salo don kawo karshen matsalar.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Jahar Kogi: An Sake Damke Fursunonin Da Suka Tsere Daga Gidan Gyaran-Hali”