April 21, 2023

Jagoran Juyin Musulunci Ya Yi Wa Fursunoni Afuwa Saboda Karamar Salla

 

A jiya Alhamis ne dai jagoran ya amince da bukatar ma’aikatar shari’ar kasar akan yin sassauci ga fursunoni da dama, da kotuna mabanbanta na kasar su ka yankewa hukunci.

Wasu daga cikin fursunonin an sassauta musu tsawon lokacin zamansu a gidan kurkuku, yayin da aka yi wa wasu afuwa baki daya.

Yawan fursunonin da afuwar ta shafa sun kai 1760.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Jagoran Juyin Musulunci Ya Yi Wa Fursunoni Afuwa Saboda Karamar Salla”