January 29, 2024

Jagoran Juyin Musulunci Ya Halarci Baje Kolin Kere-keren Da Iran Take Yi

Da safiyar yau Litinin ne dai jagoran juyin musulunci na Iran din ya halarci baje kolin kare-karen da Iran take yi a fagage mabanbanta da ake yi Husainiyyar Imam Khumaini da take a cikin birnin Tehran.

Daga cikin abubuwan da aka baje kolinsu da akwai cigaban da Iran ta samu a fagagen makamamashi, sanadarori masu alaka da man fetur da kuma magunguna. Haka nan kuma fagen abinci da noma da kayan aikin likita da ake kerawa a cikin gida.

A fagagen sana’oin hannu saka da sufuri,shimfida hanyoyin mota da na jirgin kasa da fasahar sararin samaniya ta tauraron dan’adam duk an baje kayayyakin da masana na cikin gida su ke kera.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka baje kolinsu sun kunshi babura na hawa, motoci masu aiki da wutar

©VOH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Jagoran Juyin Musulunci Ya Halarci Baje Kolin Kere-keren Da Iran Take Yi”