November 30, 2022

jagoran juyin juya halin musulunci Ya bukaci Iraki Ta Tabbatar Da Karfin Ikonta a yankin Kurdawa

Jagoran juyin musulunci na kasar Iran Ayatullah Imam Khamna’I a lokacin ganawarsa da fira ministan kasar Iraki mohammad Al’ sudani da yake ziyara a kasar iran yace duk wani abun da zai kawo cikasa kan tsaron kasar iran ba zai haifar da da mai ido ga kasar iraki ba kana ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta tabbatar da karfin ikonta a dukkan yankunan kasar musamman yankin kuradiwa mai neman yancin cin gashin kai.
Haka zalika jagoran ya ishara game da kalaman baya-bayan nan da wasu manyan jami’an kasar iraki suka yin a cewa gwamnatin bagadaza ba za ta bari a yi amfani da kasarsa wajen kai hari ga makwabtanta ba, yace abin takaici sai gas hi irin haka na faruwa a wasu yankunan kasar don haka ya bukaci gwamnatin tsakiya da shimfida karfin ikonta adukkan wadannan yankuna.

Jagoran ya kara da cewa iran ta yi amanna cewa tsaron kasar iraki daidai yake da tsaron jamuriyar musulunci ,ya jaddada cewa iran za ta mayar da martani mai tsanani kan duk wanda ya nemi ya kawo rashin tsaro a wasu kasashen larabawa.

Daga karshe Imam Khamna’I ya taya mohammad Al’sudani murnar na zabensa a matsayin sabon fira minstan kasar Iraki kana ya yi masa fatan samun nasara wajen ciyar da kasar gaba a bangarori daban-daban.

Ana sa bangaren Al’sudani ya jinjina gamd da daddiyar alakar dake tsakanin kasashen biyu yace aikin hadin guiwa tsakanin kasahen wajen kawar da kungiyar ta’adda ta Da’esh kyakkyawar alakar dake tsakaninsu

©Hausa TV.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “jagoran juyin juya halin musulunci Ya bukaci Iraki Ta Tabbatar Da Karfin Ikonta a yankin Kurdawa”