May 15, 2023

Jagoran Juyi Ya Bayyana Muhimmancin Da Littafi Na Takarda Yake Da Shi Duk Da Yaduwar Duniyar Gizo

 

Ayatullah Sayyid Imam Ali Khamnei wanda ya ziyarci bikin baje kolin littafi na kasa da kasa da ake yi a nan Tehran, ya ce; Sauya al’adun al’umma da bunkasarta yana da bukatuwa da littafi, kuma duk da cewa da akwai rubuce-rubuce a duniyar gizo, amma har yanzu littafin na takarda yana da nashi matsayin.

Dangane da buga littatafai da kuma sayar da shi cikin sauki, jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran ya ce; ya sami bayani daga ma’aikatar al’adun musulunci akan kokarin da suke yi na samar da takardu cikin sauki da hakan zai taimaka wajen yaduwar littatafan.

Ayatullah sayyid Ali Khamnei ya nuna gamsuwarsa akan yadda ya ga baje kolin da kuma nau’oin littatafan da aka kawo a wurin

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Jagoran Juyi Ya Bayyana Muhimmancin Da Littafi Na Takarda Yake Da Shi Duk Da Yaduwar Duniyar Gizo”