April 7, 2024

Jagora Yayi Afawa Ga Fursinoni Kimani 2,000 Saboda Murnar Sallah Karama

Jagoran juyin juya halin musulunci a Tehran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae yayi afuwa ga fursinoni kimani 2000 wadanda alakalin alakalan kasar ya gabatar masa, saboda bukukuwan sabuwar shekara ta kuma sallah karamamai zuwa.

A wani bayani wanda aka nakalto daga shafin hulda da jama’a na jagoran ya wallafa a safiyar yau Asabar, ya nuna cewa Alkalin alkalan kasa Hujjatul Silam Ghulam Hussain Muhsen Ijri ya gabatar da bukatar ne a wata wasikar da ya aikewa jagoran, inda a cikin ya bukaci afwa ga fursinoni 2127 a nau’in hukunci, ko sauwaka hukunci ko kuma musayar hukuncin da aka yanke masu.

Labarin ya kammala da cewa jagoran ya amince da wannan bukatar tare da bukatar a aiwatar da su a cikin gaggauwa.

©Htv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Jagora Yayi Afawa Ga Fursinoni Kimani 2,000 Saboda Murnar Sallah Karama”