May 24, 2023

​Jagora Ya Ce Majalisar Dokokin Kasar Ce Ta Ceci Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Daga Shiga Rudu

 

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminaee ya bayyana cewa Dakar da majalisar dokokin kasar ta kafa a shekara ta 2020 ce ta kubutar da kasar daga fadawa cikin rudu dangane da shirinta na fasahar Nukliya ta zaman lafiya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jagoran yana fadar haka a safiyar yau Laraba, a lokacinda yake ganawa da wasu yan majalisar dokokin kasar a nan Tehran.

Dokar wacce ta bukaci gwamnatin kasar ta takaita binciken da da hukumar IAEA take yi a a cibiyoyin Nukliyar kasar zuwa wanda ya zama lazimi kadai, da kuma gaggauta aikin gasa sinadarin Uranium saboda maida martani gas aba alkawarin da kasashen yamma da kuma Amurka suka yi a yarjeniyar JCPOA.

Imam Kjamenei ya kuma taya mutanen Iran murnar zagayowar ranar kwatar lardin Khurammashar daga hannun sojojin Sadam Husaine a yakin shekaru 8 da suka fafata da ita a kuma wani farmaki wanda aka bawa suna ‘Baitul Mukaddasi’ a lokacin.

Da wannan nasarar kuma aka kawo karshen mamayar da sojojin Iraki na lokacin suka yiwa birnin Khurramshar na tsawon kwanaki 500.

Daga karshe jagoran ya bayyana cewa dabar barun da aka yi amfani da su a farmakin baitul mukaddasi basu kai muhimmancin shahidan da aka rasa a yakin ba, don haka bai kamata a manta da wannan ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Jagora Ya Ce Majalisar Dokokin Kasar Ce Ta Ceci Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Daga Shiga Rudu”