February 6, 2024

Jagora Ya Bukaci Masu Fada Aji A Duniyar Musulmi Su Yanke Alaka Da Isra’ila

 

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce masu fada a ji na al’ummar musulmin duniya na da rawar da zasu iya takawa dangane da halin da ake ciki a Zirin Gaza, ta hanyar yanke alaka da gwamnatin Isra’ila.

A yayin wata ganawa da wani gungun kwamandoji da jami’an sojojin saman Iran a yau litinin, Ayatullah Khamenei ya yi gargadi game da “masifu na bil’adama” da ke faruwa a Gaza sakamakon goyon bayan da Amurka ke baiwa gwamnatin Isra’ila.

Ya bayyana cewa kasashe na iya matsawa gwamnatocinsu lamba don kawo karshen goyon bayan da suke baiwa gwamnatin Isra’ila.

Duk da cewa wannan mulki na “zalunci” ya salwantar da rayukan mata, da yara sama da 20,000, amma har yanzu wasu kasashen musulmi suna hulda tattalin arziki da ma ta makamai da Isra’ila, in ji Jagoran.

Ya ce : “ba wai muna nufin shiga yaki da gwamnatin Isra’ilar ba, amma muna nufin ladabtar da ita ta hanyar yanke huldar tattalin arziki da ita.

 

©Voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Jagora Ya Bukaci Masu Fada Aji A Duniyar Musulmi Su Yanke Alaka Da Isra’ila”