November 23, 2023

Jagora Ya Bayyana Cewa Kungiyar Hamas Duk Tare Da Halin Da Gaza Yake Ciki Ta Sami Nasara A Kan HKI

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta sami nasara a kan HKI a yakin tufanul Aksa da ta soma a ranar 7 ga watan Octoban da ya gabata, wannan duk tare da asarar rayukan yara, mara da sauran Falasdinawa da aka yi a wannan yakin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jagoran yana fadar haka a a yau Laraba a lokacinda yake ganawa da yan wasan mutsa jiki, jami’an ma’aikatar wasanni da sauran yan wasa a kasar a gidansa.

Ha’ila yau Jagoran ya yabawa yan wasa wadanda suka bada kyautar lambobin yabonsu ga Falasdinawa musamman a dai dai lokacinda ake yakin Tufanaul Aksa.

Daga karshen Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya kara da cewa kungiyar Hamas a matsayin wata karamar kungiyar ba kasa ba, ammam ta shiga yaki da kasa wacce take samun tallafi daga manya manyan kasashen duniya, inda daga karshe ta tilasta mata amincewa da sharuddanta kafin ta karbi yahudawan da ta yi garkuwa da su. Wannan ba karamin nasara bace, kuma manuniya ce kan cewa nan ba da dadewa ba HKI zata bace a bayan kasa. Kuma za’a kafa kasar Falasdinu mai cikekken yenci a nan gaba ba tare da dadewa ba.

 

©V.O.H

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Jagora Ya Bayyana Cewa Kungiyar Hamas Duk Tare Da Halin Da Gaza Yake Ciki Ta Sami Nasara A Kan HKI”